Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Falasdinu ta fitar da alkaluman da ba a taba jin irinsu ba na bala'in yakin da yake samun mutane a Gaza bayan watanni 11 tun farkon fara fitar da adadin rayukan da yakin ya shafa, wanda ke nuni da cewa mutane 10,000 ne suka rage a karkashin baraguzan gine-gine da kuma gawarwakin shahidai kusan 1,760 da suka kone, duka wadannan rayuka sun salwanta ne saboda anfanin da makaman da aka haramta da gwamnatin Sahayoniya ta yi akansu, wanda ke sa gawarwakin su ko ne ba za a iya gano su ba.
Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: babbar ma’aikatar agaji da
ceto ta Falasdinu, a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Gaza a
daidai lokacin da ake tunawa da ranar ayyukan jin kai ta duniya, ta yi nuni da
cewa, Hukumomin yahudawan sahyoniya sun kame ‘yan kasar Falasdinu da suka kai 8240.,
kuma babu labarin makomarsu, haka kuma gawarwakin mutane 2,210 sun bace daga
kaburburansu a zirin Gaza, kuma babu labarin gawarwakin wasu shahidai wanda
gwamnatin yahudawan sahyoniya ta ce ta yi shahadantar da su.
A cikin watanni 11 da suka wuce na yakin Gaza, Ma’aikatar agaji ta Falasdinu ta yi nasarar tattara gawarwakin shahidai 35,580 daga cikin jimillar shahidai dubu 40 da aka yi wa rajista a wannan yanki tare da mika su asibiti, amma gwamnatin sahyoniyawan ta hana ma’aikatar kaiwa ga gawarwakin wasu shahidai har guda 14,420, wadanda 4,420 ne 'yan kasar suka ciro daga karkashin baraguzan ginin, kuma gawarwakin mutane kusan 10,000 na karkashin baraguzan ginin. Haka kuma an kai gawarwakin shahidai 8,973 zuwa asibitoci.
A cewar Ma’aikatar agaji ta Falasdinu, tawagogin wannan ma’aikata sun taimaka wa mutane dubu 82 da 800 da suka jikkata da kuma iyalai dubu 25 da 430 da aka tilastawa barin gidajensu a wurare masu hadari, kuma gwamnatin sahyoniyawan a cikin watanni 11 na karshe na yakin Gaza ta jefa kusan tan dubu 85 na bama-bamai a kan mazauna yankin Zirin Gaza, wanda ya lalata fiye da kashi 80% na ababen more rayuwa na birane da kashi 90% na kayayyakin more rayuwa, kuma kashi 17% na wadannan makaman ba su fashe ba har yanzu suna barazana ga rayuwar mazauna Gaza. Ya zuwa yanzu, yara 90 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasa da ragowar makaman yahudawan sahyoniya da su kai saura.
Ita dai wannan ma’aikata ta bayyana dangane da ikrarin da gwamnatin sahyoniyawan take yi na cewa akwai "yankuna masu aminci" a zirin Gaza, da cewa gwamnatin sahyoniyawan ta tara Palasdinawa a wani yanki da ke da kashi 10.5% na yankin zirin Gaza, kuma ahakan ta ke yin iƙirarin cewa wai yana da "aminci da mutuntawa". wannda ta aikata kisan kiyashi da laifuffuka sau 21 sannan mutane 347 suka yi shahada yayin da wasu 766 suka jikkata a wadannan yankuna.
Ma’aikatar agaji ta Falasdinu ta kuma bayyana shahadar ma’aikatan ta 82 da kuma jikkata wasu 270 na daban, ta kuma ce kashi 40% na kungiyoyin wannan ma’aikata suna fuskantar hare-hare da kuma hatsarin jiki daga zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, sannan cibiyoyinta da motocin aikinta an sha kai hari akansu, tare da lalata su gaba daya, ko kuma lalata wani bangarensu.
Wannan Ma’aikata, ta yi nuni da cewa, aikin ma’aikatun jinkai na kasa da kasa shi ne taimakawa cibiyoyin agaji da samar musu da kayayyakin da za su ci gaba da gudanar da ayyukansu, idan aka kwatanta da rage rawar da kungiyoyin kasa da kasa da na MDD ke takawa wajen tallafawa ayyukan jin kai da da Ceto da kungiyar ke yi ta yi gargadi game da ci gaba da yakin kisan kare dangi da ke faruwa tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.